Nigeria ta yi watsi da sharadin Boko Haram

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Gwamnatin Nigeria ta yi watsi da sharadin da kungiyar Boko Haram ta gicciya, na sakin mayakanta kafin ta saki 'yan matan Chibok.

Ministan cikin gida Patrick Abba Moro ya shaida wa BBC cewa, kasar da wasu gwamnatocin duniya sun ayyana Boko Haram a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, saboda haka ba zai yiwu kungiyar ta gicciya wasu sharuda na sake 'yan matan da suka sace ba.

Ko da ya ke ya amince cewa tattaunawa na daga cikin sharudan cimma sulhu, amma kuma wajibi ne gwamnati ta tabbatar da doka, saboda babu wanda ya fi karfin doka.

Najeriya ta amince da tayin taimaka mata da wasu kasashen duniya suka yi, ciki har da Amurka da Birtaniya da Israila da kuma China, wajen neman 'yan matan fiye da 200 tare da ceto su.

A ciki da wajen Najeriyar ana cigaba da zanga zangar neman a ceto 'yan matan na Chibok.