'Mun samu bayanai kan 'yan matan Chibok'

Image caption Gwamna Kashim Shettima

Gwamnan Jihar Borno da ke arewacin Nigeria ya ce ya samu bayanai a kan inda 'yan mata fiye da 200 suke da 'yan Boko Haram suka sace.

Gwamna Kashim Shettima ya shaidawa BBC cewar ya mika bayanan ga sojoji don su gudanar da bincike a kai.

Shettima ya kara da cewar ba ya tunanin an ketara da 'yan mata zuwa kasashen Chadi da Kamaru masu makwabtaka da Nigeria.

Makonni hudu kenan da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata fiye da 200 a makarantarsu da ke Chibok a kudancin jihar Borno.

Abubakar Shekau na kungiyar Boko Haram ya yi barazanar sayar da 'yan matan a 'kasuwa'.

'Taro kan Boko Haram'

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya yi tayin daukar bakuncin taro kan Boko Haram a kasar sa.

Hollande ya ce "Na yi wa Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan tayin taro kan Boko Haram tare da kasashen da ke makwabtaka da Nigeria".

Hakkin mallakar hoto white house
Image caption Michel Obama ta bukaci a ceto 'yan matan

A cewarsa idan kasashen suka amince, za a gudanar da taron a ranar Asabar mai zuwa.

Kasashen da ke makwabtaka da Nigeria su ne Kamaru, Niger da kuma Chadi.

A waje daya kuma Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya ce ya amince da tayin taimakon da Firaiministan Isra'ila Benjamin Natanyahu na taimakawa wajen gano 'yan matan na Chibok.

A don haka, tawagar kwararrun yaki da ta'addanci na Isra'ila za su hadu da na Amurka da China da Birtaniya da kuma na Faransa wadanda tuni suka zo Nigeria domin wannan aiki da kuma murkushe 'yan kungiyar Boko Haram.

Karin bayani