Kura ta soma lafawa a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Salva Kiir da Riek Machar

Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar a ranar Juma'a ga alama ta fara aiki.

An ci gaba da samun tashe-tashen hankula a jihar Upper Nile mai arzikin mai a karshen mako bayan sanya hannu a kan yarjejeniyar.

Sai dai wani mai magana da yawun rundunar soji Philip Aguer ya shaidawa BBC cewa ba a sake jin wani tashin hankali ba a ranar litinin.

Jami'in kungiyar agaji ta Oxfam Colm Bryne wanda ke Juba ya ce mutane suna fata za a kawo karshen tarzomar

Ya ce "Mun san cewa an sami yan tashe tashen hankula amma ina tsammanin yarjejeniyar tsagaita wuta abar maraba ce kwarai."

Karin bayani