Amnesty ta zargi wasu kasashe da azabtarwa

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Amnesty na zargin kasashe da cin zarafin mutane

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatocin kasashen duniya da kin magance azabtar da mutane, bayan da aka shafe shekaru talatin da Majalisar Dinkin Duniya ta zartar da dokar hana gallazawa mutane a duniya ba ki daya.

Amnesty ta ce ta samu rahotanni cewa akwai gallazawa daban-daban da suka hada da fyade, da amfani da wutar lantarki, da hana bacci da kimanin kasashe saba'in da tara a duniya suke yiwa mutane.

Kungiyar ta kara da cewa azabtarwar ana yi wa wadanda ake tuhuma da aikata muggan laifuka ne, ko kuma wadanda jami'an tsaro ke zargi da aikata wani laifi, wanda a ciki har da kananan yara.

Amnesty ta ce ci gaba akan yakar azabtawa na samun nakasu a duniya saboda wasu gwamnatoci na fakewa da aikata hakan kan batun tsaro.

Karin bayani