'Chibok: 'Yan Boko Haram su zo a sasanta.'

'Yan matan Chibok da aka sace Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan matan Chibok da aka sace

Gwamnatin Nigeria ta ce a shirye take ta daidaita da kungiyar Boko Haram, dangane da musayar 'yan matan Chibok da mayakanta.

Sai dai gwamnatin ta ce za ta saurari muradin kungiyar ne kawai, idan kungiyar ta sanar da wakilan da za su wakilce ta a tattaunawar sulhun.

Ministan ayyuka na musamman na kasar, wanda har wa yau ke jagorantar kwamitin sulhu da gwamnatin ta kafa, Barrister Kabiru Tanimu Turaki ne ya shaida wa BBC hakan.

Gwamnatin ta yi zargin cewa a baya ta sha cimma irin wannan yarjejeniya da kungiyar, amma daga baya sai shugabanninta su fito suna shiriritar da maganar.

Kawo yanzu dai kungiyar ta Boko Haram ba ta mayar da murtani ba ga kiran na gwamnati.