'Wayoyi sun sa mutane sun daina barci'

Image caption Mutane na yawan yi amfani da wayoyinsu har cikin dare

Wasu masana a fannin kimiyya sun yi gargadin cewa, na'urorin zamani sun sa mutane na mantawa da muhimmancin barci.

A cewarsu amfani da kwamfuta da wayoyin komai da ruwanka da mutane ke yi na sa su yi barci kalilan, haka zalika masu aikin dare.

Masanan sun ce yin hakan na shafar kwayoyin halitta na DNA, kuma hakan kan kai ga cutar daji ko sankara da ciwon zuciya da ciwon suga da kamuwa da kwayoyin cuta da kuma teba.

Gargadin wanda aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet a watan jiya, ya nemi likitoci su dinga rubutawa mutane su je su yi barci, domin inganta lafiya.