An haifi tagwaye suna musabiha a Amurka

Hakkin mallakar hoto akron hospital
Image caption Mahaifiyarsu ta ce abin al'ajabi ne

Wasu tagwaye da aka haifa rike da hannun juna a Amurka, na numfashi da kansu bayan an cire su daga na'urar da ke taimaka wa jarirai rayuwa.

Tagwayen 'yan matan Jillian da Jenna Thistlethwaite, sun kasance a cikin mahaifa daya lokacin da suke ciki.

An haifi 'yan biyun ne ranar Juma'a a jihar Ohio, rike da hannun juna yayin da Likitoci suka fito da su daga cikin mahaifiyarsu, Sarah Thistlethwaite.

Likitoci sun ce wannan wata larura ce da ake samu a haihuwa daya cikin dubu 10.

An rika kula da Ms Thistlethwaite mai shekaru 32, a Babban asibitin Akron saboda tagwayen na cikin hatsarin hadewa ta cibiyar junansu.

Sarah ta fada wa mujallar Akron Beacon cewa rike wadannan tagwaye nata shi ne "Babban tukwici a rayuwarta".