An hallaka sojojin gwamnatin Ukraine

'Yan a ware a gabashin Ukraine Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan a ware a gabashin Ukraine

Ma'aikatar tsaro ta Ukraine ta ce sojoji 7 ne aka kashe a wani kwanton bauna da 'yan aware suka yi a kusa da birnin Kramatorsk na gabacin kasar.

Ta ce wasu 7 kuma sun samu rauni a lokacin wani hari da wasu 'yan gwagwarmaya kusan 30 suka kai.

An ce suna dauke da makaman harba gurneti da kuma masu sarrafa kansu.

Tashin hankalin ya zo ne kwana daya kafin hukumomin Kiev su shirya tattaunawar gaba da gaba, a wani kokari na kawo karshen tashin hankalin.

Sai dai da yake magana a wajen wani taron manema labarai na hadin guiwa, Pirayim Minista, Arseniy Yatsenyuk, ya ce ya rage ruwan Rasha ta kwantar da kurar tashin hankali a gabacin Ukraine.