Sojoji sun harbi motar shugabansu a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin sun harzuka ne bayan ganin gawawwakin abokan aikinsu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka yi musu kwanton bauna

Rahotanni daga Maiduguri a jihar Borno na cewa wasu sojoji da suka fusata sun harbi motar shugaban rundunar sojoji na birnin, Manjo Janar Muhammad.

Lamarin ya auku ne a ranar Laraba da safe, inda rahotannin suka bayyana cewa, sojojin sun fusata ne sakamakon abin da suka kira rashin kulawa da bukatunsu daga shugabanninsu.

A cewar rahotannin sojojin sun kuma zargi shugabanninsu da yi musu turin jeka ka mutu a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Najeriya ke bukatar a sabunta dokar ta baci a jahar ta Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Karin bayani