Wata guda da sace 'yan matan Chibok

'Yan matan Chibok 130 da kungiyar ta nuna a bidiyo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya bukaci a sake mayakan kungiyar kafin su saki 'yan matan

A ranar Laraba ne aka cika wata guda cif da sace 'yan mata dalibai fiye da 200 a makarantar Chibok da ke jihar Borno.

Gwamnatin Najeriya ta ce a shirye ta ke ta shiga sulhu da kungiyar Boko Haram da ta sace 'yan matan, idan har ta turo wakilanta.

Yayin da kasashen waje ke taimakawa Najeriya wajen gano inda 'yan matan ke boye, ministan Afrika a ofishin kungiyar Commonwealth da ke Birtaniya zai kawo ziyara Najeriya, domin ganawa da jami'an gwamnatin kasar.

Kungiyoyi da wasu daruruwan 'yan Najeriyar na cigaba da zanga-zanga da kuma zaman dirshen a wasu sassan kasar, domin karin matsin lamba kan gwamnati game da ceto 'yan matan na Chibok.

Iyayen 'yan matan dai sun ce sun shiga wani hali na ni-ya-su, saboda halin rashin tabbas da 'ya'yansu suka shiga.

Gwamnatin ta sha suka daga ciki da wajen kasar, inda tsohon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan da tsohuwar ministan harkokin wajen Amurka Hillary Clinton suka zargi hukumomin kasar da jan kafa game da batun 'yan matan na Chibok.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani