An lalata masana'antu a China

Hakkin mallakar hoto
Image caption An lalata masana'antu a China

Masu kin jinin Gwamnatin China a kudancin Vietnam sun lalata daruruwan masana'antu tare da kona akalla guda goma sha biyar.

Tashin hankalin ya biyo bayan zanga-zangar da dubban ma'aikata suka yi wadanda ke kalubalantar matakin da Beijin ta dauka na sanya wata na'urar hakar ma'adinai a cikin tekun kudancin China da ake takaddama akai.

Masu kula da masana'antu sun ce masu zanga-zangar su na kai hare-harensu ne a masana'antu mallakar China ko kuma wadanda 'yan China ne ke lura da su.

Haka kuma wani jami'in gwamnati a Taipei ya ce akalla masana'anta guda mallakar Taiwan aka lalata tare da jikkata wasu 'yan kasuwa guda biyu.

Sun kuma yi kira ga jami'an Vietnam su dauki mataki domin kawo karshen rikicin.

Karin bayani