Mutane 200 sun mutu a Turkiyya

Prime Ministan Turkiyya Racep Tayyip Erdogan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lamarin ya sa Prime Minista Erdogan daakatar da tafiyar da zai yi kasar waje.

Fiye da mutane dari biyu ne suka rasa rayukansu a wata mahakar ma'adinai a kasar Turkiya.

Da dama daga cikin wadanda suka rasun sun mutu ne sanadiyyar shakar gubar sinadirin Carbon Monoxide bayan fashewar wani abu mai matukar karfi da ke karkashin kasa.

Masu aikin ceto da ke kokarin isa ga fiye da ma'ikatan hakar ma'adinai kusan dari biyu da suka makale a kasa sun dakatar da kokarin da suke na isa wajen saboda dalilan kariyar lafiya.

Wakilin BBC yace fashewar abin ta faru ne kilomita biyu a karkashin kasa lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki tare da toshewar hanyar shakar iska.

Kuma Prime Minista Racep Tayyip Erdogan ya dakatar da tafiyar da zai yi kasar waje, a maimakon haka ya nufi mahakar ma'adinan da ke garin Soma.

Ministan makamashin Turkiyya Taniya Yeldez yace lokaci na kure musu wajen aikin ceton,a bangare daya kuma jama'a sun yi dandazo a wajen ya yin da asibitin yankin ke cike makil da jama'a.