An sanar da makokin kwana 3 a Turkiyya

wani mutum da kenan da ya tsallake rijiya da baya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Prime Minista Racep Tayyip Erdogan ya dakatar da tafiyar da zai yi don kai ziyara wurin aikin ceton.

Gwamnatin Turkiyya ta yi shelar makokin kwanaki uku a kasar bayan ma'aikatan hakar ma'adanai fiye da 200 sun mutu sakamakon fashewar wani abu da ya haddasa gobara a wata mahakar kwal da ke yammacin kasar.

Daruruwan 'yan'uwa da dangi ne cikin damuwa suka taru a kusa da mahakar da ke garin Soma yayin da ma'aikatan ceto ke zakulo gawawwaki da mutanen da suka ji raunuka.

Da dama daga cikin mamatan sun mutu ne sanadiyyar shakar gubar sinadirin Carbon Monoxide bayan fashewar wani abu mai matukar karfi da ke karkashin kasa.

Wakilin BBC ya ce fashewar abin ta faru ne kilomita biyu a karkashin kasa lamarin da ya janyo katsewar lantarki tare da toshewar hanyar shakar iska.