Chibok: APC ta soki Nigeria kan kin musaya

Malam Nasiru El-Rufa'i
Image caption Sai dai ministan yada labarai da shugaban kwamitin sulhu da Boko Haram sun ce kofar tattaunawa a bude take

Wani kusa a jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria, Malam Nasiru El-Rufa'i ya soki gwamnatin kasar kan watsi da tayin musayar 'yan matan Chibok da Boko Haram ta yi.

Inda ya ce yakamata gwamnati ta tattauna da kungiyar, ta san abin da suke so domin a ceto 'yan matan Chibok fiye da 200.

El-Rufa'i ya ce matakin gayyatar kasashen waje na taimakawa Nigeria wajen neman 'yan matan daidai ne, amma ka da su turo dakarunsu Nigeria.

Ya dora laifin tabarbarewar tsaro kan gwamnatin jam'iyyar PDP mai mulki, na sanya siyasa a kan batun Boko Haram.

Ministan cikin gida da shugaban Majalisar dattawan Najeriya sun ce gwamnati ba za ta yi musayar 'yan matan da fursunonin Boko Haram ba, saboda kungiyar 'yan ta'adda ce.