Tsawaita wa'adin dokar ta baci a Nigeria

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Laraba ne 'yan Majalisar suka kwashe sa'o'i fiye da uku suna tafka muhawara kan batun

A ranar Alhamis ne ake sa ran 'yan majalisar wakilan Najeriya za su kada kuri'a a kan bukatar da shugaba Goodluck Jonathan na neman a kara wa'adin dokar ta-baci.

'Yan Majalisar kuma za su saurari bahasi daga manyan hafsoshin tsaron kasar, kafin kada kuri'ar.

'Dan majalisa Gwani Bukar Lawal daga jihar Yobe yace ba sa so a kara dokar ta baci a Jihohin Yobe da Borno da kuma Adamawa.

Yana mai cewa babu abin da dokar ta bacin ta karawa jihohin, sai ci baya domin ana dokar ta bacin ne aka kai hare-hare akan makarantun sakandare na jihar ta Yobe har sau biyu.

Gwani ya ce Shugaba Jonathan ya sanya dokar ta baci a dajin Sambisa tun da a can kungiyar Boko Haram ta ke.