IMF ta tuhumi Mali kan sayen jirgin $40m

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mali ta shiga tattaunawar sulhu da 'yan tawayen MNLA da Azbinawa da kuma kungiyar Ansar Dine

Hukumar lamuni ta duniya, IMF ta bukaci sanin dalilan da yasa Mali ta saya wa shugaban kasar jirgi na biyu akan kudi dala miliyan 40.

Hukumar ta IMF ta kara nuna damuwa kan dala miliyan 200 na odar kaya ga hukumar tsaron kasar.

Wani kakakin IMF ya ce hukumar za ta jinkirta biyan kudaden agajin da za ta bai wa Mali, har sai jami'an kasar sun yi mata bayani.

A ranar Alhamis ne masu ba da tallafi na kasashen waje za su yi wa jami'an Mali tambayoyi, game da yadda suke kashe kudaden tallafin da ake ba kasar.

Hakan na zuwa ne shekara guda bayan Mali ta karbi kudaden tallafi da bashi na kusan $4 biliyan, domin farfado da kasar.

Karin bayani