An kai hari a kauyen Ngawo Fate a Borno

Hakkin mallakar hoto
Image caption Lokacin da aka kai harin babu jami'an tsaro a kauyen

Wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kan kauyen Alau Ngawo fate da ke jihar Borno, inda suka kona daukacin kauyen.

Mutum biyu sun mutu a harin da 'yan bindigar suka kai kan kauyen dake karamar hukumar Jere, a ranar Laraba da daddare.

Haka kuma rahotanni daga jihar Jigawa sun ce an kashe masu tayar da kayar baya 60 a dajin Lamba, da ke kusa da karamar hukumar Gwaram.

A makon jiya ne wasu mahara da ake zargin 'yan kungiyar ne suka kashe fiye da mutane 300 a garin Gamboru Ngala a jihar Borno.