Boko Haram ta gagari Jonathan - Obasanjo

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Oabasanjo ya ce ya kamata a yi sulhu da 'yan Boko Haram, kuma a murkushe wadanda suka yi kunnen-kashi

Tsohon shugaban Nigeria, Olusegun Obasanjo, ya ce matsalar Boko Haram ta gagari shugaba Goodluck Jonathan.

A wata hira da ya yi da BBC, Mista Obasanjo ya ce tuntuni ya so ya jagoranci sasantawa da 'yan kungiyar ta Boko Haram lamarin da ya kai shi Maiduguri.

Ya kara da cewa da an samu bakin zaren a wancan lokacin da tuni an kawar da matsalar.

A cewarsa, bai taba tunanin tashe-tashen hankulan da Boko Haram ta kawo za su kai Nigeria ta bukaci taimakon kasashen waje ba.

Mista Obasanjo ya jaddada cewa hanyar kawai da za a magance matsalar ita ce a zauna kan tebirin sulhu da 'yan kungiyar, sannan a yaki wadanda suka yi kunnen-kashi.

Karin bayani