Sudan za ta rataye mace saboda ridda

Image caption Hukumomi sun dauke ta Musulma saboda mahaifinta musulmi ne, amma ba a gabansa ta girma ba

An yankewa wata mata 'yar Sudan mai shekaru 27, hukuncin ratayewa bisa laifin aikata ridda, bayan ta auri wani mabiyin addinin Kirista.

Haka zalika, an yankewa mata hukuncin bulala 100, bisa laifin aikata zina saboda kotun ta ce auren na ta bai halalta ba.

Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International, ta ce Dr. Maryam Yahya Ibrahim, wadda ke da juna biyu na watanni 8, ta tashi ne a matsayin Kirista.

A karkashin tsarin shari'ar Musulunci, ba a yarda mace Musulma ta auri namiji wanda ba Muslumi ba ne, kuma irin wannan aure ko da an yi shi, bai halalta ba.