Ana ci gaba da bore a Brazil

Masu zanga-zanga a Brazil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu boren dai su na kokawa ne da yadda babu ababen more rayuwa ga talakawan kasar, da rashin aikin yi.

'Yan sandan kwantar da tarzoma a kasar Brazil sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zanga a Sao Paulo da Reo de Janeiro.

Masu zanga-zangar dai na yin boire ne saboda abinda suka kira makudan kudaden da aka kashe wajen shirya gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da Brazil ke karbar bakunci wadda za a fara a wata mai zuwa.

Dandazon mutanen na yin jefa da duwatsu tare da bakawa tayoyi wuta akan tituna tare da toshe hanyoyin wucewa.

Yawanci 'yan kasar na jin haushin an kashe biliyoyin daloli a wasan, maimakon a inganta ayyukan ci gaban al'uma kamar samar da gidaje ga talakawa.

Masu aiko da rahotanni mutanen da suka fito zanga-zangar ba su kai yawan wadanda sukai bore a shekarar da ta gabata ba.

Sai dai masu shirya boren su yi alkawarin za a yi gagarumar fitowa nan gaba kadan kafin a fara wasan kwallon kafar.

Babban birnin kasar Brazil wato Brazilia ma bai huta ba domin nan ma an gudanar da bore irin wannan da wasu biranen kasar.