Me ya hana Nigeria murkushe Boko Haram?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Shekara guda kenan da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sanya dokar ta-baci a arewa-maso-gabashin Nigeria, domin dakatar da hare-haren kungiyar Boko Haram.

Kamar yadda shugaba Jonathan ya bayyana, yace an saka dokar ta bacin don yin amfani da wasu dabaru na daban don magance hare-haren domin dawo da zaman lafiya a yankin.

Jonathan ya umarci dakarun soji su yi amfani da kowace irin hanya matukar bata kauce ka'ida ba domin murkushe ayyukan ta'addanci da na mahara.

Amma sai hare-haren Boko haram ya kara ta'azzara a watanni 12 da aka dauka ana aiwatar da dokar a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Ga misali kungiyar Boko Haram ta kai hari kan wasu barikin soji a Maiduguri da kuma tashar mota ta Nyanya a Abuja da karin wani harin a Nyanya.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Sannan kuma kungiyar kaddamar da wani mummunan hari, inda ta sace wasu 'yan mata fiye da 200, a makarantar sakandaren 'yan mata da ke Chibok, abin da ya tayar da hankalin duniya.

Baya ga nan akwai mummunan harin da ake zargin ta kai garin Gamboru Ngala dake bakin iyakar Najeriya da Kamaru, inda aka kashe mutane fiye da 300 .

Editan jaridar Daily Trust ta Najeriya Habeeb Pindiga ya ce "Lokacin da aka kafa dokar ta-bacin na yi tsammanin cewa za a yi gwaji ne, amma daga karshe naga babu wata nasara".

A tsawon lokacin da dokar ta yi aiki a jihohin uku na arewa-maso-gabashin kasar, rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane 740 a cewar wata kididdiga da Jami'ar Sussex ta kasar Birtaniya ta fitar.

Adadin yawan fararen hular da suka jikkata cikin watanni 12 ya ninka da kashi uku zuwa 2,265.

Tsaka-mai-wuya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin cewar dakarun Nigeria sun gaza

Pindiga ya ce sojoji sun tsinci kansu a cikin halin tsaka-mai-wuya.

Saboda cin zarafin jama'ar da ake zargin dakarun Najeriyar da aikatawa mutane ba su yarda da su ba, bugu da kari ba su da makamai na zamani, babu horo ga rashin basu kwarin gwiwa.

Wani jami'in sojin Birtaniya wanda ya yi aiki a karamin ofishin jakadanci kasar a Najeriya, James Hall ya ce "Matsalar gwamnatin Nigeria ita ce tana bukatar wata na'ura ce kawai da ka kunna za ta magance komai."

Ya kara da cewa "Wani babban kwamanda ya taba tambaya ta ko za mu iya sayar musu da wani inji, wanda idan mota na zuwa za ta iya sanin ko akwai dan ta'adda a ciki. "

"Na yi kokarin nuna masa cewa babu irin wannan inji, amma bai yarda ba gani kawai ya ke muna boye musu ne."

Kanal Hall mai ritaya ya kara da cewa wata matsalar ita ce Birtaniya na kaffa-kaffa wajen bayar da horo ko sayar da makamanta masu kyau.

"Mun rage yawan horon da muke bayarwa da kuma makaman da muke bayarwa."

Hukumomin kare hakkin bil'adama na Human Rights Watch da Amnesty sun soki matakan da dakarun Najeriya ke dauka.

Amnesty ta bayar da rahoton cewa kimanin mutane 600 sojoji suka kashe, a harin da aka kai barikin sojoji na Giwa da ke Maiduguri a watan Maris.

Saboda irin wannan damuwa ya sa wata doka ta Birtaniya ta haramta sayarwa Najeriya manyan makamai.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Abubakar Shekau ya ce zai sayar da 'yan matan Chibok

Mr. Hall ya yi nuni da cewa "Kuma idan ba mu bai wa dakarun Nigeria horo ba, ba za mu basu makamai ba, tun da horon ma ba za mu yi musu ba."

Dakarun Najeriya dai sun sha yabo game da irin rawar da suka taka a wasu kasashen duniya, abin da kuma tsohon sojan ya gaskata.

Sai dai ya kara da cewa "Sun rage karfin sojinsu saboda suna tsoron juyin mulki."

Amma sojin Najeriya sun musanta zarge-zargen.

Wasu dai na ganin sanya siyasa cikin lamarin Boko Haram ya kara dagula lamarin, inda hukumomi ke ganin tun da tashin hankalin ya fi kamari ne a jihohin da jam'iyyar adawa ke mulki, kambama shi kawai ake yi.

Sai dai batun sace 'yan matan Chibok fiye da 200 ya sa gwamnatin kasar ta sauya tunaninta, inda nemi taimakon wasu kasashen duniya.