Jonathan zai ziyarci Hollande a Faransa

Image caption Jonathan zai halarci taro a Faransa kan Boko Haram

A yau Juma'a ne ake sa ran shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan zai kai ziyara kasar Faransa.

Shugaban zai kai ziyarar ne don tattaunawa da takwaransa na kasar Faransa, Francois Hollande da nufin samo hanyoyin magance rikicin da Najeriya ke fama da shi sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.

Tuni dai wasu kasashen yammacin duniya da dama suka ci alwashin taimaka wa Najeriya ta wannan fuskar.

Ministan tsaro Genaral Aliyu Gusau da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Col Sambo Dasuki na daga cikin wadanda suka marawa shugaban baya zuwa Faransar.

Karin bayani