Keta hakkin bil adama a Ukraine

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakarun 'yan aware a Ukraine

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce an samu tabarbarewar al'ammura ainun game da batun keta hakkin bil adama a Ukraine.

Wani rahoto da masu binciken suka wallafa, ya ce ana samun karuwar keta doka da oda a gabashi da kudancin kasar ta Ukraine.

Rahoton ya kuma ce an karkashe daidaikun jama'a, tare da sace wasu da kuma azabtar da su, kuma galibi masu adawa da gwamnati ne suka aikata hakan a gabashin kasar.

Sai dai kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha, Alexander Lukashevich, ya ce rahoton ba shi da tushe:

Ya ce "Ya zame mana dole mu fito mu fada cewa rahoton bai nuna ainihin halin da ake ciki a kasa ba game da batun keta hakkin bil adama".

Karin bayani