India: BJP na sahun gaba

Narendra Modi ya yin kamfe Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Modi dai ya ci alwashin idan ya zama shugaabn kasa baki zai bunkasa tattalin arzkin kasar, da samar da ayyukan yi ga matasa.

Ana kidaya kuri'un da aka kada a kasar India, inda sakamakon farko ke nuna nasara ga dan takara gwamnatin hadaka ta BJP wato Narendra Modi.

Shalkwatar jam'iyyarsa da ke Delhi na cike da jama'a ana ta murna, ya yin da mutane ke kallon yadda ake kidayar kuri'un a hoton majigi, a bangare guda kuma makada na ta buga ganga suna rera wakoki.

Can a shalkwatar jami'iyyar Congress mai mulkin kasar kuwa shiru ka ke ji, a daidai lokacin da kidayar kuri'un ta nuna gagarumar tazarar da ke tsakanin jam'iyyar da ta 'yan adawa wato BJP.

Wannan dai shi ne kusan shan kaye mafi muni da ake ganoin jam'iyyar Congress ta samu a zabukan da aka gudanar a kasar.

Sama da mutane miliyan 500 ne suka kada kuri'a a kasar ta India.

Karin bayani