Shugabannin Afrika za su yaki Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP

Wasu shugabannin kasashen Afrika sun cimma yarjejeniyar yin aiki tare domin yakar kungiyar Boko Haram.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da shugabannin kasashen Nijer da Kamaru da Chadi da kuma Benin ne suka amince cewa za su yi aiki tare don yakar kungiyar.

Shugaban Faransa Francois Hollande ne ya jagoranci taron wanda ya shirya a Paris.

A wajen taron shugaban na Faransa da kuma na Najeriya sun ce yanzu an tabbatar cewa kungiyar Boko Haram na da alaka da al-ka'ida.

Shugaba Jonathan ya ce kungiyar ta wuce inda aka santa sa'adda ta kafu shekara ta 2002 a zaman kungiya mai wani ra'ayin addini na daban dake ta'addanci a cikin gida.

Ya ce zai ma fi dacewa a bayyana Boko Haram da cewa al-kaida ce a yammaci da kuma tsakiyar Afrika.

Sa'o'i kafun fara taron, an kai hare-hare biyu da ake dangantawa da Boko Haram din.

Harin farko an kai shi ne a Kamaru, na biyun kuma an kai shine a wani kauye a Najeriya, inda aka kashe mutane 11.

Karin bayani