'Yan bindiga sun kashe mutane 11 a Borno

Rahotanni daga Jihar Borno sun ce an kashe akalla mutane goma-sha-daya a wani hari da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a kusa da garin Mainok.

An kai harin ne a daren asabar, kuma cikin wadanda suka mutun harda wani yaro da mace daya.

Maharan sun tare motoci ne a daji daga gabashin garin Minok mai tazarar kilomita kusan 60 tsakanin Damatru zuwa Maiduguri.

Garin na Mainok bashi da nisa da garin Benisheik, inda a watan Satumban bara, 'yan Boko Haram suka tsare hanya suka kashe kimanin mutane 200 da suka hada da matafiya da kuma mutanen garin.

Maharan sun kuma kone garin na Benisheik.

Jihar ta Borno dai na daga cikin jahohi ukku na arewacin kasar dake karakashin dokar ta-baci.

Harin na garin Mainok na ya zo ne a dai dai lokacinda wasu 'yan bindiga suka kai hari akan wani kamfanin China a arewacin Kamaru.