An sace 'yan China 10 a arewacin Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu 'yan bindiga sun kai hari akan wani kamfanin China a arewacin Kamaru.

Hukumomin Chinar sun ce wani mutum ya samu rauni, kuma ba'a san inda wasu goma suka shiga ba, bayan da aka kai harin.

Wasu rahotanni sun ce an hallaka mutum daya.

Ganau sun ce an ji harbe-harbe tsakanin jami'an tsaro da kuma maharan, wadanda suka sace motocin kamfanin goma.

Lamarin ya faru ne a kusa da iyakar Kamarun da Najeriya, inda 'yan Boko Haram ke yin yadda suka ga dama.

Taro a Paris

Hakan ya faru ne a daidai lokacin da ake wani taron kasa-da-kasa a birnin Paris don ganin yadda za'a bullowa kungiyar Boko Haram wadda a watan jiya ta sace 'yan mata sama da dari biyu a garin Chibok dake Jihar Borno.

Cikin wadanda ke halartar taron -- wanda Faransa ta shirya -- sun hada harda Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da shugabannin Jamhuriyar Benin da na Chadi da kuma na Nijar.

Amurka da Burtaniya ma sun tura wakilai wadanda zasu duba irin aikin da kwararrunsu a Najeriya suka yi kawo wa yanzu, don gano 'yan matan da aka sacen.

Karin bayani