Najeriya: Zaben kananan hukumomi a jihar Kano

Zabe a Najeriya Hakkin mallakar hoto b
Image caption Zabe a Najeriya

Ana gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kano arewacin Nigeria, da shi ne karo na farko da za a gudanar a cikin shekaru bakwai.

Za dai a fafata ne tsakanin jami'iyyun PDP da kuma ta APC masu zazzafar hamayya da juna.

Kusan kusan hankulolin jama'a ya karkata ne kan zaben kananan hukumomi 44 da kansilolinsu,da za a gudanar a jihar.

hukumar zaben jihar ta ce ta bankado wata takardar kada kuri'u ta bogi da za a yi amfani da ita lokacin zaben, sai dai bai yi karin bayani kan ko su wa ake zargi da yunkurin amfani da su ba.

Rundunar Yansandan jihar dai ta sanar da dokar hana zirga-zirga tun daga karfe shida na safe har zuwa hudu na yamma, ta kuma ce ta samar da karin jami'anta daga jihohi makwabta don gudanar da zaben lami lafiya.

Gabanin zaben dai an sha fuskantar tashe tashen hankula har ma da asarar rayuka a lokacin yakin neman zabe, abin da ke nan ya sa wasu ke fargabar samun hargitsi a lokacin zabukan na yau.