Najeriya:Hare-hare kan hanyoyin Maiduguri

Boko Haram Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Boko Haram

A jihar Borno arewacin Najeriya ana fuskantar hare-haren 'yan Boko Haram a kan hanyoyin Maiduguri zuwa Bama da zuwa Damaturu jihar Yobe.

Maharan sun sauya sabon salon kaiwa matafiya harin ne inda sukan yi kwanton bauna a kan bishiyoyin dake bakin hanya suna bude wuta kan mafafiya.

A wasu lokutan ma su kan labe a cikin gidajen kauyukan da suka jama'a suka kauracewa saboda hare-haren

Ko a daren shekaranjiya ma an samu asarar rayukan mutane 11 yayin da da dama suka jikkata yayin wani hari da 'yan bindigar suka kai kan wasu matafiya a garin Mainok dake dake kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Jihar ta Borno dai na daga cikin jahohi ukku na arewacin kasar dake karakashin dokar ta-baci sakamakon kalubalen hare haren 'yan kungiyar ta Boko Haram dake ci gaba da dagula lissafin hukumomin.