Kwashe 'yan kasar China daga Vietnam

Zanga-zangar kin jinin 'yan kasar China a Vietnam Hakkin mallakar hoto
Image caption Zanga-zangar kin jinin 'yan kasar China a Vietnam

Kasar China za ta aike da karin jiragen ruwa biyar zuwa Vietnam don gaggauta kwashe 'yan kasar ta sakamakon tarzomar kin jinin- 'yan China da ta barke.

Hakan ya biyo bayan girke na'urorin hakar mai na Chinar a tekun kudancin kasar da kasashen biyu ke ikirarin mallaka.

Kamfanin dillancin labarai na China Xinhua, ya ce jirgin farko ya tashi daga tsibirin kudancin Hainan.

Chinan ta kwashe sama da 'yan kasarta 300 daga Vietnam din bayan da aka kashe wasu ma'aikatanta biyu a tashin hankalin.

Ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar ta China ta nuna matukar damuwarta kan lamarin tana mai cewa gwamnati a Hanoi ba ta dauki mataki a kan masu tarzomar ba.

A jiya Asabar ne dai wani jami'in gwamnatin Vietnam Laftanal Janar Hoang Kong Tu ya ce za a dau kwakkwaran mataki kan wadanda ke da hannu kan zanga-zangar.

Amma kuma masu fafitka a kasar sun sake yin kiran da ci gaba da gudanar da zanga-zangar a yau Lahadi.