'Yan tawaye sun sace sojojin Mali 24

Hakkin mallakar hoto Getty

Abzinawa 'yan a-ware a garin Kidal na arewacin Mali, sun sace sojoji 24 da ma'aikatan gwamnati hudu.

An sace su ne bayan sun je sun gana da Firaministan Malin, Moussa Mara, wanda ke ziyararsa ta farko a arewacin kasar tun bayan zamansa firaminista watan jiya.

Wakilin BBC ya ce babu tabbas a kan ko ana tsare da su ne a ofishin gwamna - wanda har yanzu ke hannun 'yan tawayen - ko kuma an dauke su zuwa wani wurin daban.

Ma'aikatan tsaron Mali ta ce soji takwas ne aka kashe, aka kuma kashe Abzinawa 28 a kabsawa a garin na Kidal, wanda wani bangarensa yana hannun 'yan tawayen ne.

An sanya dokar hana fita a Kidal yayinda kuma jirage masu saukar angulu ke ta shawagi.

Wani mazaunin Kidal din, Malam Buhari Kidal, ya gayawa BBC cewa jama'a na zaman fargaba a garin.

Karin bayani