'Yan APC sun yi zanga-zanga a Katsina

Image caption Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande

Wasu magoya bayan babbar jam'iyyar hamayya ta Najeria, APC sun ce shugabannin jam'iyyar a Katsina suna yi wa jam'iyyar zagon-kasa tare da neman yi wa janar Muhammadu Buhari kutunguilar rasa takara a badi.

Daruruwan magoya bayan jam'iyyar ta APC wadanda suka yi wata zanga-zangar lumana a gaban shalkwatar jam'iyyar da ke Katsina a ranar Lahadi.

'Ya'yan jam'iyyar sun nuna rashin amincewarsu da abin da suka kira fafutukar da Sanatocin jam'iyyar da 'yan majalisar wakilai na jiha da na kasa ke yi ta hana ruwa gudu a zabukkan shugabannin jam'iyyar da har yanzu jihar ta zamo koma-baya, sun ce dole ne a yi zabe na gaskiya.

Masu boren sun dauki wannan mataki ne bayan zaben farko na shugabannin unguwanni na jam'iyyar da aka yi cikin wani hali na rudani.

Sai dai a nasu bangaren, 'yan majalisar sun ce zargin da ake musu ba tada tushe.

Karin bayani