Apple da Google sun yi sulhu

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Samsung da Apple sun dade suna kalubalantar juna a kotu

Kamfanin Apple da na Google, sun amince su janye karar da kowannesu ya shigar na zargin juna kan satar fasaha.

A wata sanarwa da suka fitar, kamfanonin sun amince za su yi aiki tare a wasu bangarori na yi wa fasahar garambawul.

Amma yarjejeniyar ba ta hada da bayar da lasisin fasahar su ga juna ba.

Kamfanin Apple wanda ke kera wayoyin komai da ruwanka na iphones, da kuma kamfanin wayoyi da ke amfani da manhajar Android na Google, sun shigar da kararraki suna zargin juna.

A farkon wannan watan ne, wani alkali a California ya umarci kamfanin Samsung na Korea ta Kudu ya biya kamfanin Apple dala miliyan 119.6 kwatankwacin fam miliyan 71, saboda satar fasahohi biyu na Apple.

Haka kuma kotun ta umarci Apple ya biya Samsung's dala 158,000 a matsayin diyya shi ma saboda satar fasahar Samsung.

Ana sanya mahajar Andriod a sababbin wayoyi kashi 80 cikin dari da ake sayarwa kowace shekara.

Karin bayani