'Yar Iran ta sumbaci shugaban 'yan Fim

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leila Hatami

Sumbatar da wata 'yar wasan Fim ta kasar Iran Leila Hatami ta yi wa shugaban shirin karrama tauraran 'yan fim Giles Jacob domin yi masa maraba ya haifar da takaddama da cece-kuce a Iran.

Hatami ta sumbaci Jacob ne a yayin bude bikin karrama tauraran 'yan wasan wanda aka gudanar a kasar Faransa.

Mukaddashin ministan al'adun kasar ya maida martani da jan hankali masu halartar bukukuwan kasa da kasa da su yi hattara kada su batawa matan Iran suna.

Sai dai kuma a waje guda wasu Iraniyawan sun kare 'yar wasan fim din a shafukan intanet suna zargin gwamnatin da yi mata barazana.

Ita dai Leila Hatami ta yi suna musamman a rawar da ta taka a wani fim din Iran din mai suna 'The Seperation' wanda ya sami lambar yabo ta Oscar a shekarar 2012.