An gano mota da abubuwan fashewa a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mashayar da dan kunar bakin wake ya lalata a Kano

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta ce ta gano wata mota makare da abubuwan fashewa a kan titin Tafawa Balewa da ke Kano.

A cewar rundunar ta samu nasarar kwance bam din tun kafin ya fashe, saboda abubuwan fashewar masu ta'adi ne.

Hakan na zuwa ne kwana gudan bayan da wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane kusan biyar a wata mashawa da ke Sabon Gari a jihar ta Kano.

Kakakin rundunar 'yan sandan Nigeria, Frank Mba a cikin wata sanarwa, ya ce motar da aka gano kirar Mitsubishi na dauke da abubuwan fashewa kafin a samu a kwance.

Harin na Sabon Gari ya kuma jikkata mutane da dama tare da lalata wasu motoci guda biyar da ke kusa da wurin, baya ga motar dan kunar bakin. Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhalin kai wannan harin.

Karin bayani