Tashe-tashen hankula a kasar Libya

Tashin hankali a kasar Libya
Image caption Tashin hankali a kasar Libya

Gwamnatin Libya ta ce har yanzu ita ce ke rike da iko, duk da manyan hare-hare da tarzomar da ta barke a birnin Benghazi ranar Jumma'a.

A babban birnin kasar Tripoli dakarun wata kungiyar 'yan bindiga sun kai farmaki kan ginin majalisar dokokin kasar, inda aka kashe mutane biyu.

Daga bisani ne kuma kakakin wani janar din soja, ya bukaci 'yan majalisar da su mika iko ga kwamitin da aka nada don samar wa kasar sabon tsarin mulki.

Sai dai wani minista dake gwamnatin ya yi watsi da batun kana ya bukaci zaman sasantawa na kasa.

Da sanyin safiyar Litinin kuma an samu rahotannin kai hari kan filin saukar jiragen saman soji a birnin Benghazi.

An dai danganta rikicin da yunkurin da manyan kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai ke yi na dakile matakan masu tsattsuran ra'ayin addinin Islamar.