Louis van Gaal ne manajan Man U

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Louis van Gaal ne ya gaji David Moyes wanda aka kora

An bayyana Louis van Gaal a matsayin sabon manajan Manchester United tare da Ryan Giggs a matsayin mataimaki.

Louis van Gaal ya sanya hannun yarjejeniyar shekaru uku kuma zai koma jan ragamar kungiyar bayan ya jagoranci Netherlands a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Louis mai shekaru 62 ya lashe gasa tare da Ajax da Barcelona da kuma Bayern Munich.

Yace "Wannan kungiyar na cike da buri, kuma zamu hada hannu don kafa tarihi".

Manchester United ta kori David Moyes a watan Afrilu, watanni goma kacal bayan ya gaji Sir Alex Ferguson, wanda ya jagoranci kungiyar na tsawon shekaru 26.