Za a rusa jami'an gabar ruwa a Koriya ta Kudu

Shugabar Korea ta Kudu Park Geun-hye Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Mutane fiye da 300 ne suka mutu a hadarin jirgin ruwan a watan jiya

Shugaba Park Geun-hye ta Korea ta Kudu za ta rushe hukumar jami'an tsaron gabar ruwan kasar, don gaza tabukawa wajen hadarin jirgin ruwan.

A wani jawabi da ta yi ta gidan talabijin Ms Park, ta bayar da hakuri da nuna nadama kan wahalar da al'ummarta suka shiga sakamakon hadarin jirgin.

Ta ce ayyukan ceton da jami'an tsaron gabar ruwa zasu koma karkashin wata hukumar bayar da agajin gaggawa, kuma yanzu binciken da ake yi kan hadarin zai koma hannun 'yan sanda.

Shugabar ta kuma yi alkawarin kawar da rashawa da zambar da ake aikatawa tsakanin jami'an kula da harkokin jiragen ruwa da kamfanonin safarar jiragen ruwa.