UNITAD na shirin bullo da haraji kan mai

Sakatare Janar na MDD Ban Ki_Moon Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakatare Janar na MDD Ban Ki_Moon

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai lura da samar da kudade don habaka fasahar kirkira UNITAD ta ce za ta fara tattaunawa da wasu kasashen Afirka masu arzikin mai domin gabatar da wani shirin harajin musamman a kan man don kafa wani asusun Afirka domin kula da lafiya.

Shugaban hukumar Philippe Douste-Blazy ya ce hikimar ita ce domin tsakurar dan abin da bai taka kara ya karya ba, na harajin kashi goma cikin dari a kan kowace gangar mai da aka hako, wanda za a cire daga ribar da gwamnatocin suka samu.

Kasashen Najeriya da Algeria da kuma Angola su ne dai manyan kasashen Afrika masu arzikin mai.

Sai dai kuma Mr Douste-Blazy ya ce ya yi wuri ya bayyana kasashen da yake tuntuba.