An yi wa 'yan Al-Shabaab luguden wuta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Al-Shabab na Somalia

Rahotanni daga Somalia na cewa wasu jiragen saman Kenya sun yi luguden wuta a kan wani gari da ke hannun 'yan kungiyar Al-Shabaab.

Wani mazaunin garin na Jilib da ke kusa da tashar jiragen ruwa ta Kismayo ya shaidawa BBC cewa mutane uku sun rasu yayin da wasu mutanen shida kuma suka sami raunuka a harin.

A shekarar 2011 ne sojojin Kenya suka shiga Somalia domin taimakawa sojojin Somalia da na kungiyar tarayyar Afirka a yakin da suke yi da 'yan bindigar.

Lamarin ya janyo 'yan Al-Shabaab na yawaita kai hare-hare a kasar Kenya.

Karin bayani