Mutane fiye da 46 sun mutu a harin Jos

Wani soja a mota mai sulke
Image caption Jos ta dade tana fama da rikicin kabilanci da na addini

Kimanin mutane fiye da 46 ne suka mutu a wani harin da aka kai, a kusa da kasuwar Terminus a Jos da ke jihar Filato a Nigeria.

Wani dan jarida a Jos, ya shaidawa BBC cewar ya kirga gawarwakin mutane 38 a cikin asibitin Jos, a yayinda ya ce yaga an kawo wasu karin gawarwakin a lokacin da yake barin asibitin.

Rahotanni sun ce an soma zaman dar-dar a birnin, saboda matasa sun harzuka sakamakon tashin bam din.

Fashewar dai ta auku ne da misalin karfe uku na rana, a daidai lokacin da 'yan-kasuwa da sauran jama'a ke hada-hada.

Kawo yanzu jami'an tsaro ba su tabbatar da adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata a harin ba.

Birnin na jos na fuskantar rikice-rikicen addini dana kabilanci.