Ana gudanar da zabe a kasar Malawi

Image caption Ana kada kuri'a cikin kwanciyar hankali a Malawi

A Malawi ana gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisu da na kansiloli, karo na hudu tun bayan fito da tsarin siyasa mai jam'iyu da yawa.

Shekaru 21 da suka gabata ne dai aka bullo da wannan tsarin siayasa a kasar.

Shugabar kasar Joyce Banda, wadda ta zamo shugabar kasa mace ta biyu a nahiyar Afrika bayan rasuwar wanda ta gada Bingu wa Mutharika a shekara ta 2012, na tsayawa takara ne a karon farko.

Wannan shi ne na farko a tarihin kasar Malawi da za a yi zaben shugaban kasa, da 'yan majalisun dokoki da kuma na kananan hukumomi a rana guda.

Kimanin shekaru 14 kenan rabon da a gudanar da zaben kananan hukumomi a kasar ta Malawi.

Hudu daga cikin 'yan takarar da ke neman kujerar shugabancin kasar sun hada da Lazarus Chakwera, da Atupele Muluzi, da Peter Mutharika da kuma shugaba mai ci Joyce Banda.