Dokar ta-baci: Kan sanatoci ya rabu

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Tuni 'yan majalisar wakilai ta Najeriyar suka amince da bukatar shugaban kasar

Ana sa ran Majalisar dattawan Nijeriya za ta ci gaba da muhawara kan bukatar da Shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar na neman kara dokar ta-baci.

Tuni dai alamu ke nuna cewa an samu rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan majalisar, bisa dalilai na bambancin jam'iyyun siyasa da bangaranci.

Majalisar za ta jefa kuri'a kan batun idan bakin 'yan majalisar bai zo daya ba yayin muhawarar.

A makon jiya ne Majalisar Wakilan kasar ta amince da tsawaita dokar da watanni shida, a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Karin bayani