Sanusi Lamido ya fuskanci cikas a kotu

Hakkin mallakar hoto getty and reuters
Image caption Shugaba Jonathan da Sanusi Lamido na takun saka

Wata Kotun Tarayya a Abuja babban birnin Nigeria ta ce bata da hurumin sauraron karar da Malam Sanusi Lamido Sanusi ya shigar a gabanta, kan dakatar da shi da shugaba Goodluck Jonathan ya yi daga mukaminsa.

Kotun ta ce batu ne da ya shafi ma'aikaci da ubangidansa.

A don haka ta mika lamarin gaban kotun da ke sauraren kararakin al'amuran da suka shafi kwadago.

Malam Sanusi Lamido Sanusi ya garzaya zuwa kotun ne inda ya nemi ta fayyace masa a kan ko shugaba Goodluck Jonathan yanada karfin ikon dakatar da shi daga mukaminsa na shugaban babban bankin kasar ba tare da tuntubar Majalisar dokoki ta tarayya ba.

Mr Jonathan a cikin watan Fabarairu ya dakatar da Sanusi Lamido daga ofis bisa zargin abinda ya saba ka'idar aiki.

Karin bayani