CIA za ta daina fakewa da allurar rigakafi

Hukumar leken asirin kasar Amurka CIA
Image caption Hukumar leken asirin kasar Amurka CIA

.Fadar gwamnatin Amurka ta ce hukumar leken asirin kasa CIA ba za ta sake yin amfani da shirin allurar rigakafi wajen fakewa don yin aikin leken asiri ba.

Matakin ya zo ne bayan korafe-korafe daga kwararrun jami'an lafiya na Amurka a kan yadda hukumar ta yi amfani da shirin kula da lafiya a Pakistan wajen farautar Osama bin Laden.

A shekarar 2011 hukumar ta CIA ta yi kokarin daukar kwayoyin halitta daga yaran da ta yi imanin suna da nasaba da Osama bin Laden, ta hanyar allurar riga kafin cutar hanta.

Tun daga wannan lokaci yan Taliban na Pakistan suke kai hari akan ma'aikatan rigakafin shan Inna inda suke cewa yan koren leken asiri ne

Karin bayani