An kashe mutane 17 a Alagarno na Borno

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Rahotanni sun ce an kashe akalla mutane 17 a wani hari da aka kai a garin Alagarno da ke jihar Borno a arewacin Nigeria.

Bayanai sun nuna cewar an kona garin kurmus da ke karamar hukumar Askira Uba wadda ke makwabtaka da garin Chibok inda aka sace dalibai fiye da 200 makonni shida da suka wuce.

Wannan harin na zuwa ne kwana guda bayan wasu tagwayen bama-bamai sun hallaka mutane fiye da 118 a Jos babban birnin jihar Filato.

Kawo yanzu ana ci gaba da tono gawarwaki a baraguzan gine-gine a kasuwar da bam din ya fashe a Jos.

Wani wakilin BBC ya ce idan har Boko Haram ce ta kai hari a Jos, to hakan tamkar sako ne ga hukumomi a Nigeria cewar za su iya kai hari a duk inda suka so a lokacin da suka ga dama.

Karin bayani