Boko Haram: Shin ina Nigeria ta dosa ne ?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Shin wai ina Nigeria ta dosa ne, ganin irin munana hare-haren da ake kaiwa a yankuna daban daban na kasar babu kakkautawa.

A cikin 'yan kwanaki kadan an kashe mutane da dama tare da jikkata daruruwa da kuma barnata dukiya.

Daga harin bam a Jos da ya kashe mutane akalla 122 zuwa na Kano da mutane kimanin shidda suka mutu, zuwa sace 'yan matan Chibok fiye da 200 da har yanzu ba a jin komai a kansu ba, lamarin sai kara muni yake yi.

Wani wakilin BBC ya ce idan har Boko Haram ce ta kai hari a Jos, to hakan tamkar sako ne ga hukumomi a Nigeria cewar za su iya kai hari a duk inda suka so a lokacin da suka ga dama.

Sojojin kasar sun gaza kare fararen hula musamman a yankin arewa maso gabashin Nigeria duk da alkawuran da suka dauka na cewar suna tura karin dakaru don shawo kan matsalar.

A baya Boko Haram ta ce za ta kafa kasa ce mai bin tafarkin shari'ar musulunci, amma kuma a yanzu hare-haren kungiyar na shafar Musulmai da Kirista.

Shugaba Goodluck Jonathan da sauran manyan jami'an gwamnati sun ce suna aiki domin tabbatar da tsaro, sai dai kuma a zahiri babu abinda ake gani ya sauya dangane da munanan hare-haren 'yan Boko Haram.

Wannan lamarin dai ya zama mai matukar firgitarwa a Nigeria.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin da aka kai a Jos a kasuwar Terminus
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan matan Chibok da aka sace
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabani sun sha alwashin yaki da Boko Haram.

Karin bayani