eBay ya bukaci a sauya kalaman sirri

Shafin intanet mai gwanjon kaya na eBay, ya bukaci masu mu'amala da shi su sauya kalmomin sirrinsu, bayan masu satar bayanai sun shiga kundin bayanansa.

eBay ya ce kundin bayanan na dauke da kalmomin sirri da ranar haihuwa da lambobin wayoyin salula da na email da adireshin akwatin gidan waya na mutane.

Kamfanin ya ce bashi da hujjojin da ke nuna cewa, masu satar bayanan sun samu cimma bayanan katin lamuni, ko kuma shigarsu ta kai ga yin wata hada-hadar da ba bisa ka'ida ba.

Hakkin mallakar hoto ebay
Image caption Mutane na sayan kaya ta shafin haka kuma suna iya tallata hajarsu

Kamfanin ya ce masu satar bayanan sun samu shiga kundin shafinsa a karshen watan Fabairu da kuma farkon Maris ta hanyar amfani da bayanan wani ma'aikacin eBay.

Jami'an tsaro da kwararru na taimakawa kamfanin wajen binciken lamarin.