An kashe 'yan Taliban 32

Mayakan kungiyar Taliban Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar Takiban ta dade ta na kai haare-hare a sassa daban-daban na kasar Afghanistan

Jami'ai a kasar Pakistan sun ce wani hari ta sama ya hallaka masu tada kayar baya 32 a arewacin Waziristan kusa da iyakar kasar da Afghanistan.

Wadanda aka tabbatar da mutuwarsu a harin mafi girma da aka kai a mafakar masu tada kayar bayan. manyan masu fada a ji ne na kungiyar Taliban.

Dubban 'yan Pakistan ne dai suka rasa rayukansu a hare-haren bama-bamai da harbin kan mai uwa da wabi tun lokacin da kungiyar Taliban ta fara kaddamar da hare-harenta akan gwamnatin kasar a shekarar 2007.

A baya dai gwamnatin kasar ta sha kaddamar da hare-hare akan 'yan Taliban din, sai dai a yanzu ta bude kofar tattaunawar sulhu da su.