Ana gwabza fada a Kidal a arewacin Mali

Sojoji a Kidal Hakkin mallakar hoto
Image caption Sojoji a Kidal

'Yan tawaye dake rike da muhimmin garin Kidal a arewacin Mali sun fatattaki sojojin gwamnati wadanda suka yi kokarin sake kwace garin.

Wani wakilin BBC a Mali yace sojojin gwamnatin sun nemi mafaka a wani sansani na Majalisar Dinkin Duniya.

Tun farko dai a yau an bada labarin barin wuta a garin na Kidal.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon, ya yi kiran a tsagaita wuta nan take.

A bara dakarun Faransa sun jagoranci farmakin da ya kai ga murkushe masu fafutukar Musulunci a arewacin Malin.

To amma a wasu yankuna masu kishin Islamar da Abzinawa 'yan aware sun cigaba da kai hare-hare.